A cikin rahoton da ya gabatar, babban sakataren Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da manufar farfado da yankunan karkara, wadda ta kasance karon farko cikin rahotannin jam'iyyar. Bisa wannan manufa, kasar Sin za ta tsara, ta kuma kyautata tsarin dunkulewar bunkasar birane da yankunan karkara wuri guda da kuma manufofin da abin ya shafa. Kasar Sin za ta gaggauta aikin zamanantar da ayyukan gona da yankunan karkara, sannan za a kara tsawaita wa'adin amfani da gona bisa kwangila har tsawon shekaru 30, ta yadda za a iya tabbatar da muradun manoma. Bugu da kari, za a kafa tsarin zamani da ya shafi aikin noma da sarrafa amfanin gona da cinikin amfanin gona. Kasar Sin, za ta ci gaba da goyon baya da karfafa zukatan manoma wajen raya ayyukansu, ta yadda za su kara samun yawan kudin shiga, da kuma kyautata ka'idoji da dokokin tafiyar da harkokin yankunan karkara. (Kande Gao)