A cikin rahoton da ya gabatar, babban sakataren Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, raya sha'anin ba da ilmi don kara karfin kasar Sin wani babban aiki ne na farfado da al'ummar Sinawa. Ya ce dole ne batun ilimi ya sha gaban komai. Kuma ya kamata a sa kaimi ga raya aikin ba da ilmin kyauta a birane da yankunan karkara baki daya, da bada muhimmanci ga samar da ilmi a yankunan karkara, da raya aikin ba da ilmi kafin shiga makaranta, da ba da ilmi ga masu bukata ta musamman, da kuma ba da ilmi ta Intanet. Haka kuma za a gaggauta kafa jami'o'in da suka fice, da kuma kyautata tsarin samar da kudin karatu, ta yadda matasan birane da yankunan karkara za su samu damar samun ilmi yadda ya kamata. (Kande Gao)