Rahoton ya bayyana cewa, ya zuwa shekarar 2035, kasar Sin za ta zamanintar da tsarin gurguzu. Za a samu babban ci gaban tattalin arziki da kimiyya da fasaha da kuma al'adu, da raya kasa da gwamnati da zamantakewar al'ummar kasar bisa dokoki, da kafa tsarin sarrafa harkokin kasa da zamanintar da kasa. A lokacin, jama'a za su yi rayuwa mai wadata, da yawan mutanen da suka samu matsakaicin kudin shiga ya karu sosai, da rage gibin dake tskanin birane da kauyuka da kuma rayuwar jama'a, da samar da hidima a zamantakewar al'umma cikin adalci, da kyautata ingancin muhalllin da ake ciki, da kuma kusan cimma burin raya kasar Sin mai kyaun gani. (Zainab)