#JKS19#Kasar Sin za ta sassauta manufofin sa ido kan kasuwanninta
Cikin rahoton da babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a wajen taron wakilan jam'iyyar karo na 19 dake gudana a birnin Beijing, ya ce kasar Sin za ta karbi tsarin bayyana fannonin da aka hana zubawa jari a fili, ta yadda za a samu damar kawar da ka'idojin da ya hana samun kasuwa ta bai daya, da yin takara cikin adalci tsakanin kamfanoni daban daban. Sa'an nan za a iya taimakawa kamfanoni masu zaman kansu wajen raya kansu, da kara janyo hankalin sassa daban daban domin su taka rawa a harkar cinikayya. Haka zalika za a yi kokarin rusa tsarin babakere, da magance yanayi na kashin dankali a kasuwa, da barin karin mutane don su shiga ayyukan samar da hidima.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku