in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19#Kasar Sin za ta kara bude kofa
2017-10-18 11:38:46 cri

Cikin rahoton da babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya gabatar wajen taron wakilan jam'iyyar dake gudana a birnin Beijing na kasar, ya ce za a dora muhimmanci kan aiwatar da shawarwarin "Ziri daya da Hanya daya", da bin manufar tattauna shirin tare, da ginawa tare, gami da moriya tare, don kara yin hadin gwiwa da fannoni daban daban a kokarin kirkiro sabbin fasahohi, ta yadda za a kafa wani tsari na bude kofa wanda zai hada hanyoyin kasa da hanyoyin teku, da sanya a rika yin cudanya tsakanin yankuna gabas da na yamma.

Xi Jinping ya ce za a kara raya kasa ta hanyar cinikayya. Sa'an nan za a samar da sauki ga ayyukan ciniki da zuba jari masu inganci, da kara bude kofa ga kasashen waje a fannin sana'ar samar da hidima, da kokarin kare hakkin 'yan kasuwa na kasashen waje. Ban da haka, za a baiwa yankunan ciniki cikin 'yanci karin damar aiwatar da gyare-gyare bisa radin kansu, da nazarin yiwuwar bude tashar ciniki cikin 'yanci. Haka zalika, za a sa kaimi ga hadin gwiwar da Sin take yi tare da kasashe daban daban a fannin masana'antu, ta yadda za a kafa wata yanar gizo ta fuskar ciniki, da zuba jari da hada-hadar kudi, da samar da kayayyaki, da kuma ba da hidima, wadda za ta amfanawa daukacin kasashen duniya.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China