Wannan tunani, a cewar Xi Jinping, ya nuna wata fahimta mai zurfi kan ainihin ka'idojin da ake bi yayin da ake gudanar da mulki karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis, da raya tsarin gurguzu, da raya zaman al'umma, da dai sauransu. Sa'an nan tunanin ya sheda cewa, za a gina wani zaman al'umma mai walwala a kasar Sin zuwa shekarar 2020. Kana a tsakiyar karnin da muke ciki, za a yi kokarin cimma burin raya kasar ta Sin don ta zama wata babbar kasa mai karfi dake bin tsarin gurguzu, wadda ke da cigaban tattalin arziki, da dimokuradiyya, da cigaban fannin al'adu, da daidaituwar al'umma, da kyan muhalli, da kuma fasahohi na zamani.(Bello Wang)