in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19#Kasar Sin ta shiga sabon zamani
2017-10-18 10:10:06 cri

A cikin rahoton siyasarsa, babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya ce, sakamakon kokarin da ake yi cikin dogon lokaci ya sa, gurguzu mai halin musamman na kasar Sin ta shiga sabon zamani, wanda ya zama sabon mafari ne wajen raya kasar Sin.

Mista Xi ya kara da cewa, a wannan sabon zamani, jama'ar Sin za su ci gaba samun nasara ta fuskar raya gurguzu mai halin musamman na kasar Sin. Jama'ar Sin za su tabbatar da zama a matsayin al'umma mai wadata, tare da raya kasar Sin na gurguzu mai karfi da zamani. Jama'ar Sin za su samu wadata duka. Al'ummar Sin za su cimma burinsu na samun farfadowa. Kasar ta Sin za ta kara bada gudummowa ga kasashen duniya da ma jama'ar duniya baki daya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China