#JKS19#Kasar Sin ta fid da mutane fiye da miliyan 60 daga kangin talauci cikin shekaru 5 da suka wuce
Xi Jinping, babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, ya furta a wajen bude taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19, wanda ke gudana a halin yanzu a birnin Beijing na kasar Sin, inda ya bayyana cewa, jam'iyyar tana bin manufar kula da jama'a, kokarinta na rage talauci a kasar ya samu nasarori masu yawan gaske cikin shekaru 5 da suka wuce. Ya ce tsakanin wadannan shekaru, an tsame mutane fiye da miliyan 60 daga kangin talauci, haka zalika ana rage yawan al'ummar dake fama da talauci da fiye da mutane miliyan 10 a kowace shekara. Hakan ya kasance wata babbar nasara ce da ba'a taba ganin irinta ba a tarihin kasar, in ji shugaba Xi.(Bello Wang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku