in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19# Sin ta gudanar da manufofin diplomasiyya a dukkan fannoni a shekaru 5 da suka gabata
2017-10-18 09:50:52 cri
Yayin da babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping yake jawabi a gun babban taron wakilan jam'iyyar karo na 19, ya bayyana cewa, Sin ta gudanar da manufofin diplomasiyya na musamman a tsakanin manyan kasashen duniya cikin shekaru 5 da suka gabata, an kafa tsarin diplomasiyya dake shafar dukkan fannoni, ciki har da aiwatar da shawarar "ziri daya da hanya daya", kafa bankin zuba jari ga ayyukan more rayuwa na Asiya, da yin kira ga kafa tsarin buri daya na dan Adam da sauransu, ta haka an daga mutuncin kasar Sin da karfin yin kira ga kasa da kasa a fadin duniya, kuma ta samar da sabuwar muhimmiyar gudummawa ga shimfida zaman lafiya da samun ci gaba a duniya. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China