in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta bukaci a kara martaba alaka tsakaninta da Amurka
2017-08-07 09:22:23 cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya jaddada bukatar dake akwai, ta karfafa mutunta juna ta hanyar shawarwari tsakanin Sin da Amurka.

Wang Yi wanda ya bayyana hakan a jiya Lahadi, ya ce daukar wannan mataki baya ga alfanunsa ga kasashen biyu, a hannu guda na shaidawa duniya irin nasarar da sassan biyu ka iya samu a nan gaba.

Ministan wanda ya bayyana hakan yayin ganawarsa da sakataren wajen Amurka Rex Tillerson a gefen taron ministocin wajen kasashen gabashin Asiya, da ma sauran tarukan masu ruwa da tsaki dake gudana a birnin Manila na kasar Philippine. Ya ce cikin shekaru 40 da suka gabata, Sin da Amurka sun cimma nasarar dakile fito na fito, da aiwatar da manufofin hadin gwiwa.

Ya ce daya daga matakai mafiya muhimmanci da kasashen biyu ke dauka domin tabbatar da hakan shi ne, aiwatar da manufar kasar Sin daya tak a duniya, da ma yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda uku da kasashen biyu ke aiwatarwa.

A nasa bangare kuma, Mr. Tillerson, cewa ya yi Amurka da Sin, a matsayinsu na manyan kasashen duniya dake sahun gaba ta fuskar tattalin arziki, na da rawar takawa wajen kawar da tashe tashen hankula da rikice rikice, lamarin da ke da tasirin gaske ga kasashen biyu, da ma sauran kasashen duniya baki daya ta fuskoki da dama. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China