A cikin rahoton siyasarsa, babban sakataren Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya ce, cikin shekaru 5 da suka wuce, JKS ta tsaya kan daukar tsauraran matakan tafiyar da harkokinta da kuma sa ido kan 'yan jam'iyyarta. JKS ta bukaci dukkan 'ya'yanta su sauke nauyin da ke wuyansu ta fuskar siyasa, ta yadda dukkansu za su kara karfafa aniyarsu da halayarsu a matsayin 'yan JKS. Har ila yau, JKS ta yi ta kyautata tsarin ka'idojinta, inda ta mai da hankali kan warware batutuwan da suka fi jan hankalin jama'a da yin barazana ga yadda take mulkin kasa. Babban Sakataren ya kara da cewa, JKS ta kara kai kaimi wajen ci gaba da farauta tare da gurfanar da dukkan wadanda suka aikata laifin cin hanci da rashawa, inda ya ce ta kuma samu gagarumar ci gaba a wannan aiki, kuma za ta ci gaba da gudanar da shi. (Tasallah Yuan)