in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
#JKS19# JKS ta samu manyan nasarori ta fuskar tattalin arziki
2017-10-18 09:43:47 cri

A cikin rahoton siyasarsa, babban sakataren jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya ce, a shekaru 5 da suka wuce, yayin da aka gaza farfado da tattalin arzikin duniya, JKS ta tsaya kan sabon tunanin raya kasa, ta sauya hanyar raya kasa, ta yadda kasar Sin ta samu manyan nasarori ta fuskar tattalin arziki.

Jimillar GDP ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan dubu 80, kuma yawan gudummowarta kan bunkasa tattalin arzikin duniya ya wuce kashi 30 cikin dari. Kasar Sin ta yi ta kyautata tsarin tattalin arzikinta, sabbin masana'antu sun samu ci gaba sosai. Kasar ta kara azama kan raya aikin gona na zamani. Ta kuma samu sakamako mai kyau wajen gabatar da shawarar "ziri daya da hanya daya" da dai sauransu. Har ila yau kasar ta Sin ta samu manyan ci gaba ta fuskar kimiyya da fasaha, kamar dakin gwaje-gwaje na Tiangong a sararin samaniya, da na'urar bincike cikin teku mai suna Jiaolong, da dai makamantansu. Bayan haka kuma, kasar Sin tana kan gaba a duniya a fannonin yin ciniki da kasashen ketare, zuba jari a waje, da kuma musayar kudaden da aka adana. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China