Dan jaridar DRC: Ya kamata a maida jama'ar Afirka su kara sanin tsarin siyasar Sin
Dan jarida na jaridar "Le Potentiel" na jamhuriyar demokuradiyyar Congo DRC Cyprien Kapuku, wanda ya zo birnin Beijing don watsa labarai game da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 19, ya bayyana a jiya ranar 16 ga wata cewa, a halin yanzu jama'ar kasashen Afirka sun fi son kasar Sin a fannin tattalin arziki, jama'ar kasashen Afirka da dama ba su fahimci tsarin siyasar kasar Sin ba. Ya ce, ya kamata 'yan jarida daga kasashen Afirka su yi kokarin maida jama'ar kasashen Afirka da su kara sanin tsarin siyasar kasar Sin da ba da fifiko kansa a wannan fanni. (Zainab)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku