in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya bukaci a kara hada kai tsakanin jam'iyyar CPC da sauran jamiyyun siyasar kasar
2017-10-15 17:49:54 cri
Xi Jinping, shugaban kasar Sin kana sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar (CPC), yayi kira da a kara samar da hadin kai tsakanin jam'iyyar kwaminis CPC wacce ke jan ragamar shugabancin kasar, da sauran jam'iyyun siyasar kasar Sin don yin aiki tare da nufin cimma burin mafarkin Sinawa na samun cigaban kasa.

A wata sanarwa da aka fitar a yau Lahadi, shugaba Xi yayi wannan kira ne a lokacin taron da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC ya shirya don jin ra'ayoyin 'ya'yan jam'iyyun da ba na kwaminis ba, a shirye shiryen rubuta rahoton babban taron CPC karo 19, wanda ake saran fara shi daga ranar 18 ga watan Oktoba.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China