Kafin isowar su Beijing, wakilan na jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin sun shiga wurare daban-daban na kasar don gudanar da bincike, inda suka saurari ra'ayoyi da shawarwarin 'yan jam'iyyar da na jama'a, domin gabatar da su ga taron da zai gudana.
A ganin wadannan wakilan, kasar Sin tana cikin wani lokaci mai muhimmanci, inda take kokarin gina wata al'umma mai walwala da neman cika burinta na raya kasa da kyautata zaman rayuwar jama'a. Saboda haka, wannan muhimmin taro da za a kira zai taimakawa jama'ar kasar Sin a kokarinsu na raya kasa.
Rahotanni sun ce, ya zuwa karfe 8 da daren jiya Lahadi agogon Beijing, tawagogin wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin fiye da 10 ne sun iso birnin.(Bello Wang)