A daidai wannan lokaci, gidan rediyon kasar Sin wato CRI zai yi amfani da harsunan Sinanci da Ingilishi da na Rasha don watsa labaran bikin kai tsaye ta rediyo, da wasu shafukan intanet na CRI, ciki har da chinaplus.cri.cn, da kuma manhajar ChinaRadio da dai sauransu.
Baya ga haka, za a watsa labaran bikin kai tsaye ta wasu manhajoji na ChinaNews da ChinaTV da dai sauransu, har ma da dandalin sada zumunta na gida da na waje, kamar Facebook da Twitter da Weibo da kuma WeChat, cikin harsuna 40 da suka hada da Hausa da Sinanci da Ingilishi da Faransanci da dai sauransu, (Bilkisu)