Dukkan tawagogi 38 na babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 sun iso birnin Beijing da yammacin jiya Litinin domin halartar taron dake karatowa.
Tawagogin na wakiltar lardunan kasar Sin 31 da sassan kwamitin tsakiya na jam'iyyar da na gwamnatin tsakiya da masana'antu da ke karkashin gwamnatin tsakiyar da na sojojin 'yantar da al'umma da 'yan sanda da kuma mambobin jam'iyyar a yankin Taiwan.
Sama da wakilai 2,200 da aka zaba daga cikin sama da mambobin jam'iyyar miliyan 89 dake fadin kasar ne za su halarci taron dake gudana sau biyu cikin shekaru 10, inda za a bude na wannan karon a gobe Laraba.
Wakilan za su tattauna kan rahoton kwamitin tsakiya na jam'iyyar na 18 da rahoton nazarin ayyukan ladaftarwa na hukumar tsakiya da kuma yi wa kundin tsarin jam'iyyar garambawul.
An sa ran taron zai kuma bayyana sabon shugabancin jam'iyyar tare da tsarin raya kasa na shekaru 5 masu zuwa. (Fa'iza Mustapha)