in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
NPC da CPPCC da majalisar gudanarwa za su hada gwiwa don samun nasarar taron CPC
2017-10-17 09:25:33 cri

Manyan kusoshin kwamitin din din din na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin NPC, da majalisar zartaswa ta kasar sun gudanar da taro a jiya ranar Litinin domin sake nazartar manufofin da aka fitar a yayin taro na 7 na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin na 18.

Majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin CPPCC ita ma ta gudanar da makamancin wannan taro kan batu iri daya.

Kana an gudanar da wani taro daga ranar 11 zuwa 14 ga watan Oktoba a nan birnin Beijing, inda aka mayar da hankali ne wajen nazartar halin da ake ciki, kuma an yi tattaunawa mai zurfi kan muhimman batutuwa da nufin tunkarar babban taron CPC karo na 19 da za'a fara shi daga ranar 18 ga wannan wata.

Firaiministan kasar Sin Li Keqiang shi ne ya jagoranci taron na ranar Litinin na manyan kusoshin majalisar gudanarwar kasar, inda aka umarci bangarori daban-daban na majalisar zartaswar kasar da su tafiyar da harkokin gudanar da shugabanci bisa tanade-tanaden da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis CPC ya amince da su.

An kuma umarci jami'an da su kasance masu da'a, da sanin ya kamata, kana su guji alakanta kansu da al'amurran da suka shafi rashawa.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China