in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta kalubalanci matakin Trump game da shirin nukiliyarta
2017-10-14 12:03:44 cri
Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya soki matakin da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka game da yarjejeniyar da kasashen duniya suka cimma game da shirin nukliliya da makamai masu linzami na Iran.

A wani jawabin da ya yi kai tsaye ta gidan talabijin bayan furucin da Trump ya yi game da sabon matakin da Amurka ta dauka kan Iran, Hassan Rouhani ya ce ba zai yiwu Trump ya yanke shawarar janyewa daga yarjejeniyar shi kadai ba.

Ya ce mai yuwa ne, Donald Trump bai san cewa daftarin ba wai yarjejeniya ce tsakanin Amurka da Iran kadai ba, ta yadda zai yi yadda ya ga dama da ita.

Ya kara da cewa, furucin Trump ya nuna cewa yarjejeniyar ta fi batutuwan da ya furta a lokacin da yake yakin neman zabe karfi, yana mai cewa, shugaban na Amurka ya gaza tuntubar sauran bangarorin dake cikin yarjejeniyar game da matakin da ya dauka.

Shugaban na Iran ya jadadda cewa, Iran za ta martaba yarjejeniyar nukiliyar matukar an kiyaye muradu da hakkokinta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China