Babban darektan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya (IAEA) Yukiya Amano ya bayyana a jiya Jumma'a cewa, Tehran tana baiwa hukumarsa hadin kai wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.
Matakin da Amurkar ta dauka bai yiwa kawayenta na yankin Turai da ma wadanda ke yankin tekun Atilantika dadi ba.
Jim kadan bayan sanarwar ce, sai kasashen Burtaniya da Faransa da Jamus suka fitar da wata sanarwar hadin gwiwa, inda suka bayyana cewa, su kam suna nan daram a kan wannan yarjejeniya, kuma ba sa tare da Trump a kan wannan mataki.
Ita ma ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha, ta bayyana cewa, babu wata kasa da za ta yiwa harkar diflomasiyar duniya barazana, kuma irin wannan mataki ba zai je ko'ina ba. (Ibrahim Yaya)