Shugaba Rouhani ya bayyana cewa, tabbatar da yarjejeniyar batun nukiliya ta kasar Iran yana da nasaba da mutuncin kasashen da suka sa hannu da kuma imanin kasa da kasa. A halin yanzu, sauran kasashen da suka sa hannu kan yarjejeniyar ba su amince kasar Amurka da ta janye daga yarjejeniyar ba, kasashe kalilan ne suka nuna goyon baya ga kudurin da Amurka ta yi.
Bayan da shugaba Trump ya hau kujerar shugaban kasar Amurka, ya nuna ra'ayi mai tsanani ga kasar Iran, kana ya ce Amurka za ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliya ta Iran, amma kasar Iran ta jaddada cewa, ba za ta amince da sake yin shawarwari ba. Kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun yi hasashe cewa, shugaba Trump zai sanar da sabbin manufofin da zai aiwatar kan kasar Iran, ciki har da kin amincewa da Iran din ta bi yarjejeniyar batun nukiliyata, kana zai mika rokon mayar da sakawa Iran takunkumi ga majalisar dokokin kasar Amurka. (Zainab)