A 'yan shekarun nan, Saudiyya da Iran sun samu sabanin ra'ayi game da wasu batutuwan da suka shafi Siriya da Yeman da kuma yaki da kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi. Ko a watan Janairun bara, gwamnatin Saudiyya ta kashe 'yan kasar Iran da aka yi zarginsu da kasancewar 'yan ta'adda da dama, ciki har da wani malamin darikar Shi'a, abun da ya sanya jama'ar kasar Iran suka yi zanga-zanga. Daga bisani kuma, Saudiyya ta katse huldar diflomasiyya da Iran. (Murtala Zhang)