in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran: Ba za a sake sansantawa kan yarjejeniyar JCPOA ba
2017-10-06 12:42:05 cri

Shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran Ali Akbar Salehi ya bayyana a jiya Alhamis cewa, ba za a sake cimma wata sasantawa game da yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma tsakanin kasar ta Iran da wasu manyan kasashen duniya a shekarar 2015 ba.

Ali Akbar Salehi wanda ya bayyana hakan a birnin Rome, fadar mulkin kasar Italiya, ya ce, kasarsa ta sha nanata cewa, bakin alkalami ya riga ya bushe game da wannan yarjejeniya.

Tun farko sai da ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zarif ya yi gargadin cewa, Tehran za ta martaba tanade-tanaden dake cikin yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma ne idan har ragowar bangarorin da wannan batu ya shafa suka martaba kushin yarjejeniyar.

Rahotanni na nuna cewa, yarjejeniyar tana fuskantar rugujewa, sakamakon wata takaddama da ta kunno kai tsakanin Amurka da kasar ta Iran.

A wani jawabi na baya-byanan da ya gabatar a gaban babban taron MDD, shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da aka cimma a matsayin abin kunya.(Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China