in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ba za ta dakatar da inganta karfin kiyaye tsaron kasar ba
2017-09-24 14:19:59 cri
Ministan harkokin tsaron kasar Iran Amir Hatami ya bayyana jiya Asabar cewa, duk da irin barazanar da wasu kasashe ke nunawa, kasar Iran ba za ta dakatar da inganta karfinta a fannin kiyaye tsaro ba.

Hatami ya yi jawabi ne game da batun gabatar da sabbin makamai masu linzami da kasar Iran ta yi inda ya nuna cewa, kasar Iran ta inganta karfin kiyaye tsaronta ciki har da makamai masu linzami don tabbatar da zaman lafiya da zaman karko a yankin, da magance rikice-rikicen da masu tsattsauran ra'ayi ke haddasawa.

Gidan rediyon kasar Iran ya gabatar da wani bidiyo a daren ranar 22 ga wata, inda aka shaida Iran ta harbi sabon makami mai linzami na Khorramshahr cikin nasara. Bisa labarin da gidan telebijin na kasar Iran ya bayar, an ce, zangon da makamin zai iya ci ya kai kilomita 2000, wadanda za su iya daukar makamai da dama, za a yi amfani da su ba da jimawa ba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China