Adadin ya ninka har sama da sau uku na yawan kudaden da kamafnin ya adana na asali wanda yawansa ya kai dala biliyan 249 a lokacin da ya adana kudaden shekaru 10 da suka gabata. Jarin ya karu cikin sauri lamarin da ya baiwa kamfanin damar zama kamfani na biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya duba da yawan kudin da kamfanin ke da shi na SWF, in ban da kudaden tsimi na fansho na gwamnatin Norway wanda yawansa ya tasamma dala trillion guda a watan jiya.
Kamfanin kula da hannayen jarin kasar Sin CIC ya samar da karin kashi 14.35 bisa 100, daga hannayen jarin da ya zuba a kasashen ketare wanda ya kai kashi 5.51 bisa 100.
Janar manajan kamfanin CIC Tu Guangshao, ya bayyana cewar, idan aka kwatanta da ragowar hukumomin gudanar da al'amurran kudi, babbar nasarar da suka samu shi ne, sun samu goyon baya daga bangaren kasuwannin kasar Sin.
Zuwa karshen shekarar 2016, kusan kashi 50 na hannayen jarin CIC na kasashen waje ya shafi hada hadar kamfanoni masu zaman kansu ne, sai kuma sabbin hanyoyin tattalin arziki dake bi masa baya, da kudaden shigar da ake adana su, sai kudaden ajiya da sauransu. Kusan kashi biyu bisa uku na hannayen jarin an gudanar da hada hadarsu ne a ketare.
Tu ya ce, bunkasuwar kamfanin kula da hannayen jarin na Sin nan da shekaru 10 masu zuwa zai ta'allaka ne da irin kokarin da ake wajen zuba jari karkashin sabon fasalin tattalin arzikin kasar Sin wanda ake sa ran zai iya taimakawa bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya.
Tu ya kara da cewa, CIC zai ci gaba da jajurcewa wajen kulla kyakkyawar dangantakar cinikayya a kasuwannin cikin gida da ketare. (Ahmad Fagam)