Kasar Sin za ta cimma burin samun ci gaban tattalin arziki na kimanin kashi 6.5 cikin dari a bana
Shugaban hukumar kididdiga ta kasar Sin mista Ning Jizhe ya ce, babu matsala, kasar Sin za ta iya cimma burin samun bunkasar tattalin arziki na kimanin kashi 6.5 cikin dari a bana, kuma mai yiwuwa ne za a samu sakamako mafi kyau.
Ning ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru na ofishin majalisar gudanarwar kasar Sin da aka shirya a yau Talata, inda ya kara da cewa, yanayin da tattalin arzikin kasar ke ciki bai sauya ba. (Bilkisu)