Wata sanarwar da majalisar ta fitar na nuna cewa, shirin yin gyare-gyaren da aka gwada a sabon yankin Pudong na birnin Shanghai, ya banbanta takardar iznin tafiyar da harkokin kasuwanci da lasisin yin kasuwanci, sannan ya takaita bayar da sabbin takardun iznin tafiyar da harkokin kasuwanci.
Sanarwar ta kara da cewa, yanzu haka shiyoyin cinikayya marasa shinge guda 10 dake sassa daban-daban na kasar, ciki har da wadanda ke garuruwan Tianjin, da Chongqing da lardunan Liaoning da Zhejiang za su fara aiwatar da shirin yin gyare-gyaren. Ana fatan shirin yin gyare-gyaren zai mayar da hankali wajen kawar da duk wasu shingaye game da samun iznin tafiyar da harkokin kasuwanci, amma kuma zai kara sanya ido da yin musayar bayanai.
A cikin shekaru biyar din da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta samarwa kamfanonin gida da na wajen yanayin kasuwancin da ya dace, ta hanyar samun takardun iznin tafiyar da harkokin kasuwanci cikin sauki, da rage biyan kudaden rajista da ayyukan hidima na zamani, a wani mataki na sakarwa kasuwa mara. (Ibrahim)