in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Botafogo ta kammala wasanni 17 ba a samu nasara a kan ta ba
2017-09-21 09:26:30 cri
A yanzu haka kungiyar Botafogo dake buga wasanni a rukunin kwararru na kasar Brazil, na matsayi na 5, maki 4 kasa da matsayin da ta kai a baya, duk da nasarar da ta samu kan takwarar ta ta Santos da ci 2 da 0, yayin wasan da suka buga a filin wasa na Rio de Janeiro. Da wannan nasara dai Botafogo ta kammala wasannin ta 17 ba a ci nasara a kan ta ba, ta kuma cika maki 41.

Yanzu haka dai Botafogo da Santos, na jiran wasan kusa da na kusa da na karshe, wanda za su buga a Laraba, a fafutukar da ake yi domin lashe kofin Copa Libertadores.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China