170831-Ghana-na-shirin-fafatawa-da-Congo-a-wasan-neman-gurbin-shiga-gasar-cin-kofin-duniya-zainab.m4a
|
A shekara mai zuwa ne dai za a buga gasar ta cin kofin duniya, wanda hukumar FIFA ke shiryawa a kasar Rasha.
Tuni dai kocin Black Stars Kwesi Appiah, ya gayyaci 'yan wasa 24 domin karawar wadda za ta wakana a filin wasa na birnin Kumasi a ranar Juma'a, bayan kuma kwanaki 4 kasashen biyu su hadu a birnin Brazaville, domin buga wasa zagaye na biyu.
A wasan horo na ranar farko, 'yan wasa 11 sun taka leda karkashin kulawar koci Kwesi Appiah. Ana kuma sa ran ganin karin 'yan wasan da aka gayyata a raneku masu zuwa.
Kungiyar Black Stars dai na neman gurbin gasar cin kofin duniya a karo na 3 a jere, kuma a yanzu tana da maki daya a wasanni biyu da ta buga a rukunin E. A daya hannun kuma, Masar za ta kara da Uganda a wannan rukuni, a ranar 31 ga watan nan na Agusta.