Yanzu haka dai an damka aikin horas da 'yan wasan kasar ga Moses Basena da Fred Kajoba, bayan da kocin kungiyar Milutin Sredojevic ya ajiye aikin sa cikin makon jiya.
Hukumar ta FUFA ta kuma ce, ta bude kofa ga masu sha'awar karbar aikin horas da 'yan wasan na dindindin, domin baiwa kwararrun kociya damar karbar ragamar kungiyar a nan gaba.
Sredojevic dai ya ajiye aikin horas da 'yan wasan na Uganda ne, sakamakon zargin da ya yiwa FUFA, na kin biyan sa wasu hakkokin sa na aiki. To sai dai kuma shugaban FUFA Moses Magogo, ya dora alhakin hakan ga gwamnatin kasar, wadda a cewar sa, ba ta kula da harkar kungiyar kwallon kasar yadda ya kamata.
Yanzu dai Basena da Kajoba ne za su jagoranci kungiyar zuwa zagayen karshe, na yunkurin samun gurbin shiga gasar cin kofin kwallon kafar Afirka na badi, inda Ugandan za ta fafata da Rwanda da Masar cikin wannan wata na Agusta, da kuma farkon watan Satumba mai zuwa.(Saminu Alhassan)