Ofishin yada labarai na gwamnatin Libya mai matsuguni a birnin Tripoli ya bayyana cewa, karkashin wannan yarjejeniyar dai, za a dawo da 'yan gudujn hijirar Tawergha zuwa gida.
Jami'ar MDDr tana ganin nasarar sasantawar a matsayin wata dama ta samar da wani ginshi ga al'ummomin tare da kawo karshen matsalar da 'yan gudun hijirar ke fuskanta.(Ibrahim)