in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojoji hudu sun mutu sakamakon harin da aka kai wa wata tashar bincike da ke Somaliya
2017-09-18 13:37:32 cri

Wani jami'in kasar Somaliya ya bayyana jiya Lahadi cewa, da safiyar wannan rana wasu dakaru sun kai farmaki kan wata tashar bincike dake yankin Beledweyne da ke tsakiyar kasar, lamarin da ya haddasa mutuwar sojojin gwamnati hudu.

Jami'in mai suna Mahad Yusuf, ya ce dakarun sun kai harin ne ba zato ba tsammani, da karfe biyar na safe na wannan rana bisa agogon wurin, kana suka fafata har tsawon rabin sa'a da jami'an tsaro. Yusuf ya kara da cewa, gwamnatin yankin ce ta kafa wannan tashar bincike don samun kudin shiga daga ababen hawa dake wucewa.

Bugu da kari ya ce, wasu mutanen da suka jikkata a yayin dauki ba dadin an riga an kai su asibiti. Mazauna wurin na bayyana cewa, sun ji amon bindigogi kafin fitowar rana.

Bisa labarin da kafofin watsa labarai na wurin suka bayar, an ce, kungiyar al-Shabaab ta kasar Somaliya sun shelanta cewa, sun kashe sojojin gwamnati 6 a lokacin fafatawar.

Kungiyar al-Shabaab ta kasar Somaliya, kungiya ce ta masu tsatsauran ra'ayi da ke da nasaba da kungiyar al-Qaeda, ta kuma sha kai hare-haren ta'addanci a kasar Somaliya da sauran kasashen da ke makwabtaka da ita.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China