Yayin wani biki da ya gudana a Monrovia babban birnin Liberia, MDD ta bada lambar yabo na wanzar da zaman lafiya ga jimilar 'yan sandan kasar Sin dari da arba'in, wato tawagar 'yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Sin na hudu, da aka tura Liberia tun watan Satumban 2013.
Tawagar 'yan sandan ta bar kasar Sin a watan Maris din 2016 domin aikin tsawon shekara guda, inda aka dora mata nauyin tabbatar tsaro a Monrovia. ( Fa'iza Mustapha)