in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar Liberia ta bukaci a gudanar da zabe mai 'yanci da adalci a kasar
2017-09-12 09:35:17 cri
Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf, ta jaddada bukatar gudanar da sahihin zabe mai 'yanci da adalci a kasarta, ranar 10 ga watan Oktoba da ke tafe.

Shugaba Sirleaf ta bayyana haka ne a jiya Litinin, yayin da take jawabi ga jama'a a hedkwatar kwamitin zaben kasar dake Monrovia, fadar mulkin kasar.

A cewar shugabar, wannan zabe zai tabbatar da ko kasar Liberia za ta samu damar ci gaba da kokarin gina kanta da raya dimokuradiya.

Kasar Liberia ta yi shirin gudanar da babban zabe a ranar 10 ga wata mai zuwa, inda za a yi zaben shugaban kasa gami da 'yan majalisar wakilai.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China