in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabar kasar Liberia ta yi kira da ake sake fasalin AU dan inganta hadin kai
2017-07-05 09:45:53 cri
Shugabar kasar Liberia mai barin gado Ellen Johnson Sirleaf, ta yi kira da a sake fasalin tarayya Afrika domin inganta hadin kai a nahiyar.

Da take jawabi yayin kammala babban taron kungiyar karo na 29, wanda ya gudana daga ranar 27 ga watan Yuni zuwa jiya 4 ga wata a Addis Ababa babban birnin kasar Habasha, Ellen Sirleaf ta bukaci a sake yi wa kungiyar garambawul, ta yadda za ta tabbatar da aiwatar da ajandar 2063 mai nufin samar da ci gaba mai dorewa a nahiyar.

Shugabar ta Liberia ta kuma yabawa AU kan kudrinta na ciyar da nahiyar gaba cikin sauri. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China