Gwamnatin kasar Sin ta kebe wa sashen ilimin kasar tsabar kudi har Yuan triliyan 3.6 a shekarar 2015, wato karin kaso 10 cikin 100 ke nan a ko wace shekara.
Wata sanarwar hadin gwiwa da ma'aikatun ilimi da na kudi da kuma hukumar kididdiga ta kasar suka fitar a jiya Alhamis, ta nuna cewa,Yuan triliyan 2.92 na wadannan kudade sun fito ne daga baitulmalin kasar, adadin da ya kai kaso 4.26 cikin 100 na GDPn kasar.
Mahakuntan kasar Sin sun shafe shekaru hudu a jere, tun daga shekarar 2012 suna zuba sama da kaso 4 cikin 100 na GDPn kasar a sashen ilimi.(Ibrahim)