in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwmanatin Amurka za ta sanar da janyewa daga shirin yaki da sauyin yanayi na tsohon shugaban kasar
2017-10-10 10:15:38 cri
Shugaban hukumar kare muhalli ta Amurka EPA Scott Pruitt, ya ce a yau Talata ne zai sanar a hukumance, da janyewa daga tsarin yaki da sauyin yanayi domin rage fitar da iskar dake gurbata muhalli na tsohon shugaban kasar Barack Obama.

Yayin wani jawabi da ya yi ta gidan talabijin jiya a Kentucky mai arzikin kwal, Scott Pruitt ya ce an riga an kawo karshen rikici kan makamashin kwal.

A nasa bangaren, shugaban hukumar EPA a zamanin Shugaba Obama kuma wanda ya fitar da tsarin wato Gina McCarthy, ya bayyana cikin wata sanarwa cewa, janyewa daga shirin ba tare da wani wa'adi ko kudurin rage iskar da ke gurbata muhalli ba, ba mataki ne na ci gaba ba.

A watan Oktoban 2015 ne gwamnatin Obama ta fitar da tsarin, wanda ya nemi tashoshin sarrafa kwal su rage yawan iska mai gurbata muhalli da suke fitarwa ya zuwa shekarar 2030 da kaso 32, daga matakin da aka sanya a shekarar 2005. Sai dai, sakamakon kuri'ar da kotun kolin kasar ta kada daga bisani ya sa an jingine shirin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China