in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Trump ya fadada haramcin shigowa kasarsa kan DPRK, Venezuela da Chadi
2017-09-25 11:02:04 cri
A jiya ne shugaba Donald Trump na kasar Amurka ya kara sanya baki daga kasashen Koriya ta arewa daga gabashin Asiya da Veneuela daga yankin Latin Amurka da kuma kasar Chadi daga yankin tsakiyar Afirka cikin wadanda aka kara haramtawa shiga kasar ta Amurka.

A halin da ake ciki kuma, shugaba Trump bai kawar da dokar nan da ta haramtawa 'yan kasashen Iran, Libya, Somaliya, Syria da Yemen shiga kasar, dokar da wa'adinta ke shirin karewa a jiya Lahadi kana ya dage takunkumin da Amurkar ta kakabawa Sudan.

Bayanai na nuna cewa, a ranar 18 ga watan Oktoba mai kamawa ne aka sa ran sabuwar dokar za ta fara aiki, har illa masha allahu.

Fadar Amurka ta White House ta bayyana cewa, sanarwar shugaban ba ta da wani bambanci da doka. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China