in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan mutanen da suka mutu da jikkata sakamakon rikicin dakaru a yammacin Libya ya karu zuwa 13
2017-09-18 13:48:19 cri

A ranar Lahadi 17 ga watan nan ne aka yi wani dauki ba dadi mai tsanani tsakanin dakaru a birnin Sabratha da ke yammacin kasar Libya, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5, yayin da wasu 8 suka jikkata.

Wani jami'i a ma'aikatar tsaron birnin ya bayyana cewa, da karfe shida na safen ranar ne sojojin rundunar dake yaki da IS, da dakarun da ke karkashin jagorancin kwamitin kula da harkokin soja na birnin Sabratha, suka yi dauki ba badi, inda suka yi amfani da kanana da matsakaitan makamai wajen fafatawa da juna har tsawon kimanin awoyi 5.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China