in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangaren masana'antun kasar Sin ya ci gaba da samun tagomashi a watan Satumba
2017-09-30 12:59:06 cri
Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta ce Bangaren Masana'antun kasar ya samu tagomashi cikin sauri fiye da ko yaushe cikin shekaru sama da 5 da suka gabata, inda ya kara karfawawa bangaren tattalin arzikin kasar.

Alkaluman dake nuna yawan kayayyakin masana'antun kasar da ake saye, ya kai maki 52.4, wanda ya karu akan maki 51.7 na watan Augusta, inda ya kai mataki mafi koli da ya taba kai wa daga watan Mayun 2012.

Makin ya dara 50 na nuni da tagomashi yayin da kasa da hakan ke nuni da koma baya.

babban jami'in kididdiga na hukumar Zhao Qinhe, ya ce wannan makin na nuni da dorewar ci gaba da aka samu a bangren masana'antun, ya na mai alakanta sakamakon da karuwar bukatar kayayyaki daga ciki da wajen kasar da kuma saurin bunkasar kamfanonin fasaha.

Jami'in ya ce karuwar sayen kayayyakin abinci da na sha da tufafi gabanin hutun kasa na kwanaki 8 da za a yi da bikin tsakiyar lokacin kaka, sun yi tasiri akan alkaluman. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China