Ministan wanda ya bayyana haka a jiya Juma'a yayin wani taron manema labaru, ya ce tallafawa manoma samun karin kudi shiga shi ne babban aikin hukumar, inda ya ce alkaluman da aka samu cikin wadannan shekaru 5 sun nuna cewa, hakar ta cimma ruwa.
A cewar jami'in, kudin shiga da manoman kasar Sin suke samu ya karu da kashi 47.4% a cikin shekaru 4 da suka gabata. Kuma an fi samun karuwar kudin shigar ne a yankunan dake fama da talauci, inda yake karuwa da kashi 10% a kowace shekara.
Ministan ya kara da cewa, ta wanna hanya, kasar Sin ta samu damar rage adadin al'ummarta dake fama da talauci, da kusan miliyan 13 a kowace shekara, ya na mai alakanta wannan ci gaba, da kokarin gwamnatin kasar na rage gibin dake tsakanin birane da yankunan karkara. (Bello Wang)