Kotun dai ta yanke hukuncin cewa, 'yan uwan Omar al-Abed ciki har da iyayensa sun san abin da dan nasu yake shirin aikatawa, amma suka kasa sanar da mahukuntan kasar Isra'ila.
Ana zargin cewa Omar Al-Abed ya shiga gidan Halamish ne dake yammacin birnin Ramallah inda ya kashe iyalan uku ta hanyar daba musu wuka, ciki har da mahaifi da 'yarsa da kuma dansa guda.
A hannu guda kuma, kotun ta yanke wa mahaifin Omar din wato Abd al-Jalil hukuncin daurin watanni biyu a gidan yari. Mahaifiyarsa Ibtisam ta shaidawa manema labarai cewa, ta gamsu da hukuncin zaman gidan yari na wata guda da aka yankewa dan nata. Yayin da 'yan uwansa maza da kanwansa kuma aka yanke musu hukuncin zaman gidan yari na watanni takwas.
A ranar 16 ga watan Yulin da ya gabata ne dai, mahukuntan Isra'ila suka rushe gidan iyalan al-Abed mai hawa biyu dake kauyen Kobar a tsakiyar gabar yammacin kogin Jordan. (Ibrahim Yaya)