in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Abbas ya jaddada muhimmancin rukunonin zaman lafiyar Isra'ila a yunkurin zaman lafiya na Falestinu da Isra'ila
2017-08-21 13:57:12 cri
Shugaban Falesdinawa Mahmoud Abbas, ya jaddada cewa, runkunonin zaman lafiya na kasar Isra'ila suna taka muhimmiyar rawa wajen yunkurin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Falestinu da Isra'ila.

Abbas ya bayyana haka ne a yayin da yake ganawa da tawagar jam'iyyar New Moment ta kasar Isra'ila a jiya Lahadi a birnin Ramallah dake yammacin kogin Jordan.

A nasa bangare, shugaban jam'iyyar ta New Moement Zehava Gal-On ya ce, bisa matsayin su na abokan zaman lafiya, babu banbancin ra'ayi a tsakaninsu da shugabannin Falestinu, suna kuma dagewa ga manufar kawo karshen ayyukan mamaye, tare kuma da kafa kasa mai 'yancin kai, bisa iyakar kasa da aka shata a shekarar 1967.

Jam'iyyar New Moement na da sassaucin ra'ayi a Isra'ila, tana kuma dora muhimmanci kan wasu batutuwa da suka shafi tabbatar da zaman lafiya da Falesdinu, da kare hakkin bil Adama, da 'yancin addinai, da kiyaye muhalli da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China