Amurka ta dakatar da tallafin wasu kudade har dala miliyan 96 ga kasar Masar, da karin wasu kudaden tallafawa ayyukan sojin kasar har dala miliyan 195, bisa zarginta na take hakkokin bil Adama. Mahukuntan Amurkar dai sun ce za su dakatar da wannan tallafi ne, har sai Masar ta kyautata tsarin dimokaradiyyar ta.
To sai dai kuma wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Masar din ta fitar a jiya Laraba, ta bayyana rashin jin dadin kasar da daukar wannan mataki, tana mai cewa Amurka ta gaza fahimtar muhimmancin dake akwai, na tallafawa wanzuwar managarcin yanayi na zaman lafiya a Masar, tare da watsi da kyakkyawa, kuma dadaddiyar dangantakar dake tsakanin sassan biyu.(Saminu Alhassan)