Shugaban hukumar lura da ingancin sufurin jiragen sama na kasa da kasa (ICAO) Olumuyiwa Benard Aliu, ya yaba da matakan tsaron da aka dauka a filayen jiragen sama na kasar Masar wanda ya yi daidai da tsarin gudanarwa na kasa da kasa.
Kamfanin dillancin labarai na MENA na kasar, ya ambato cewa firaministan kasar Masar Sherif Ismail, ya yi wata ganawa da shugaban na ICAO, inda Aliu, ya yaba da irin rawar da hukumomin kasar Masar suke dauka wajen samar da cibiyoyin ba da horo ga jami'an dake aiki a filayen jiragen saman kasar.
A lokacin ganawar tasu, Ismail ya nanata muhimmancin shirin da Masar ta yi wajen samar da cibiyoyin ba da horo a fannin sufurin jiragen saman kasar.
Aliu ya isa birnin Cairo a ranar Lahadi, domin halartar tattaunawar shiyya ta kwanaki 3 wanda aka tsara gudanarwa a yankin Red Sea resort na birnin Sharm al-Sheikh, wanda za'a fara a ranar Talata.
Taron wanda za'a gudanar mai taken "Shirin samar da tsaro a fannin sufurin jiragen sama (GASeP): Jadawalin bunkasa ingantaccen tsaro a fannin sufurin jiragen sama na Afrika da gabas ta tsakiya. "
Ana sa ran za'a nazarci matakai da za su kara tabbatar da tsaron harkar sufurin jiragen saman, kuma za'a aiwatar da dokokin inganta sha'anin sufurin jiragen sama na Afrika da gabas ta tsakiya.(Ahmad Fagam)