Ma'aikatar harkokin wajen Masar ne ta bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ta nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Najeriya da al'ummar kasar a kokarin da suke yi na yaki da ta'addanci, kana ta bukaci kasa da kasa da su goyi bayan kokarin da Najeriyar ke yi wajen dakile ayyukan ta'addanci da masu tsattsauran ra'ayi.
Kasar Masar ta aike da sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, tare ta fatan samun sauki ga wadanda suka jikkata.
A ranar Talata ne aka kadddamr da tagwayen harin kunar bakin wake a jihar Borno dake arewa maso gabashin Najeriya, inda mutane 28 suka rasa rayukansu, wasu mutane sama da 80 suka samu raunuka. (Ahmad Fagam)