in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan ta kara wa'adin shirin tsakaita bude wuta a yankunan da ake fama da tashin hankali zuwa watan Disamba
2017-10-09 09:40:00 cri
Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ya zartar da dokar tsawaita shirin tsakaita bude wuta a dukkan yankunan da ake fama da tashin hankali a kasar zuwa watan Disamba, kamfanin dillancin labaran kasar SUNA shi ne ya rawaito.

Sanarwar ta kara da cewa, manufar tsawaita wa'adin tsakaita bude wutar shi ne, domin a samu damar yin shiryen shiryen shiga tattaunawar sulhu a yankuna biyu, wadanda suka hada da kudancin Kordofan da yankin tekun Blue Nile, a matsayin yunkurin da gwamnati ke yi na cimma burin samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da kuma lalibo hanyoyin farfado da ci gaban kasar.

Gwamnatin Sudan ta kaddamar da yaki da sashen arewa na 'yan tawayen (SPLM) dake yankunan kudancin Kordofan da tekun Blue Nile ne tun a shekarar 2011, an sha yunkurin shirya tattaunawa a lokuta daban daban a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha da nufin kawo karshen tashin hankalin da ya ta'azzara a sassan kasar, sai dai yunkurin bai kai ga samun nasara ba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China