in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta sanar da soke takunkumin tattalin arziki da ta sanya wa Sudan
2017-10-07 12:48:20 cri

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta sanar a jiya cewa, kasar ta tsai da kudurin soke takunkumin tattalin arziki da ta sanya wa Sudan, ganin yadda gwamnatin Sudan din ke kokarin daukar matakai a fannoni daban daban.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Madam Heather Nauert ta bayyana cewa, Amurka ta tsai da wannan kuduri ne saboda a cikin watanni tara da suka gabata, gwamnatin Sudan ta dauki matakan a zo a gani a fannonin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita bude wutar yaki a yankunan dake fama da rikici a kasar da kara amincewa da ayyukan jin kai, tare da hada gwiwa da Amurka a fannin yaki da ta'addanci. Amma a waje daya kuma, Amurka ta jaddada cewa, gwamnatin Sudan na bukatar karin kokari don cimma burin samun zaman lafiya mai dorewa daga dukkan fannoni a kasar.

Har ila yau a jiyan, ma'aikatar harkokin wajen Sudan ta sanar da cewa, gwamnatin kasar ta yi marhabin hannu biyu biyu da matakin na Amurka. Kana ta dauki batun a matsayin babban ci gaba ta fuskar huldar da ke tsakanin kasashen biyu. Ta ce, tattaunawa mai amfani da kasashen biyu suka yi a fili ba tare da boye komai ba, ta taimaka sosai wajen samun wannan kyakkyawan sakamako.

Tun a shekarar 1993, Gwamnatin Amurka ta shigar da kasar Sudan cikin jerin kasashe masu goyon bayan ta'addanci, sa'an nan ta fara sanya mata takuntumi ta fuskar tattalin arziki a shekarar 1996.

A ko da yaushe, gwamnatin Sudan na fatan kyautata dangantakar da ke tsakaninta da Amurka, amma Amurka ta ce ba zai yiwu ba, har sai Sudan din ta aiwatar da Yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Sudan ta kudu daga dukkan fannoni, tare da warware rikicin Darfur.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China