Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar jiya, ta jadadda kudurin gwamnatin kasar na yaki da matsalar safarar bil Adama bisa dokokin kasar, musamman dokar yaki da safarar bil adama ta 2014, baya ga kudurinta na amfani da dokokin kasa da kasa dake da alaka da mastalar.
Ma'aikatar ta bayyana wasu matakan da Khartoum ta dauka na yaki da safarar bil adama, ta na mai cewa, gwamnatin ta kafa cibiyoyin karba da kula da mutanen da aka yi safararsu tare da samar musu da tallafi.
Har ila yau, ta jadadda kudurin kasar na ci gaba da hada hannu da al'ummomin kasashen waje wajen yaki da matsalar.
A ranar 30 ga watan Satumban da ya gabata ne fadar white House ta Amurka, ta ayyana tare da kara wasu kasashe 6 da suka hada da Sudan da Iran da Venezuela da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Equatorial Guinea da kuma Sudan ta kudu cikin jerin kasashen da suka gaza yaki da safarar bil Adama. (Fa'iza Mustapha)