in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sudan na fatan Amurka za ta dage mata takunkumi cikin sauri
2017-10-02 12:31:45 cri

Gwamnatin Sudan, ta bayyana fatan ganin Amurka ta dade mata takunkumin karya tattalin arziki da cinikayya nan da ranar 12 ga watan nan na Oktoba.

Cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a jiya Lahadi, karamin ministan harkokin wajen kasar ta Sudan Attal-Mannan Bakheet, ya ce an kammala duk wata tattaunawa tsakanin Khartoum da Washington.

Sanarwar ta kara da cewa, kwamitocin da suka nazarci sabanin dake tsakanin sassan biyu, sun tattauna game da dukkanin batutuwan da suka dace, an kuma mikawa Amurka bayanai masu nagarta, wadanda ake fatan za su ba da damar dagewa Sudan din takunkumi.

Amurka dai ta tsawaita lokacin nazari game da yiwuwar dagewa Sudan din takunkumi da watanni 3 tun daga watan Yulin da ya gabata. Takunkumin harkokin kasuwanci da aka kakabawa Sudan din, na da nasaba ne da matakan kare hakkokin bil Adama da kasar ke aiwatarwa, da sauran batutuwa da dama wadanda Amurkar ta nuna rashin gamsuwa da su.

A ranar 13 ga watan Janairun farkon shekarar nan, tsohon shugaban Amurka Barack Obama, ya gabatar da umarnin shugaban kasa guda biyu, wadanda ke kunshe da kudurin sokewa Sudan din takunkumin karya tattalin arziki. Umarnin ya kunshi ware kwanaki 180, domin nazarin halin da kasar ke ciki, da ma kokarin da mahukuntan ta suke yi na martaba hakkokin bil Adama da yaki da ta'addanci kafin aiwatar da soke takunkumin.

Kaza lika umarnin ya tanaji yiwuwar baiwa bankunan kasar damar ci gaba da gudanar da huldodi da takwarorin su na Amurka.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China